Monday, 14 January 2019

Yadda ake hada kafi kaza



Daga jin sunan kafi kaza kasan akwai dadi a cikinsa, shi dai wannan abinci da hausawa suke yi abinci ne na marmari ko ince kayan kwalan da maqulashe irin nasu na hausawan. Yadda ake hada wannan abu ba abu bane mai wuya, amma in ana maganar dadi to kafi kaza shi ne kan gaba wajan kayan jin dadi ga talaka kai har ma da masu kudin. An`a hada kafi kaza da abubuwq kamar haka; kifi ko kan kifi, amma mutane da dama sunfi yinsa da kan kifi, sai quli-quli, tumatir da kuma attaruhu, sai kuma man gyada.




1. Da farko mai girki zata ɗakko, kifin ta ko kan kifin ta wanke shi, sannan ta gyara shi, wato ta cire masa qaya da sauran abubuwan da ba'a buqata.

2. Zata daka quli-qulinta a turmi, sai ta kwashe shi, ta zuba kayan miyan nata a cikin tirmin ta dake su, ta dan daddaka kan kifin shima, kar ta bari ya dagargaje.

3. Sai ta ɗakko kaskonta ta ɗora shi a wuta, ta zuba mai bada yawa ba, ta ɗan soya kifin nata, sannan sai ta zuba kayan miyan a ciki,  tana yi tana juyawa, har su fara soyuwa. Sannan ta zuba quli-qulin har ta ga alamar sun soyu.  kada ta bari du ƙone, domin zai saka yayi baƙi, kuma yaƙi yin daɗi.

4. Sai ta sauke shi, ta jira ya huce, sannan a fara ci.
Dadi kan dadi.

No comments:

Post a Comment