Monday, 14 January 2019

Yadda ake cin maki mai yawa a jarrabawar jamb

 

Ko wane mutun a duniya yana so ya samu nasara a duk abinda ya saka gaba a rayuwarsa. Sanin kanmu ne cewa jarrabawa tana da wahala da shiga rintsi ga wanda zaiyi ta. Saboda haka ya zama dole ga wanda zaiyi ya shirya matuqa domin gudun samun matsala. Jarrabawar jamb jarrabawa ce mai matuqar muhimmanci, wanda sai mutun yaci sannan zai samu damar shiga jami’a. Anan zamuyi bayanin hanyoyin da mai yin jarrabawar zai bi domin samun nasara.

1. Da farko ya zama wajibi ga mai son cin jarrabawar jamb ya haqura da wani jin dadin sa na wasu loqutan, ya bawa loqacin karatunsa muhimmanci sosai.

2. Daga cikin matsalolin da suke damun daliban Nigeria shine, basa son karatu, to in har kana son kaci jarrabar jamb, ya zama dole ka bawa karatu kaso 70% daga cikin loqutanka na ko wacce rana.

3. Ka raba kanka da mutanan daba karatu bane a gabansu, ka samu abokan karatu, wadanda ko yaushe karatu ne a gabansu, ba shagali da shashanci ba.
4. Ka haqura da baccin safe, don wannan loqaci ne mai matuqar muhimmanci, malamai da yawa sunyi bayani a kan wannan loqacin.

5. Ka yawaita amsa tambayoyin baya da aka tambaya (past question), domin suna taimakawa sosai wajan cin jarrabawar. Ko ince sune jigon cin jarrabar ma.

6. Abu na qarshe kada mutun ya shiga da wasu kaya na satar amsa, ka yi qoqari wajan saurin amsa tambayoyin, domin saurin yana taimaka kwarai da gaske.

In dai kukabi wadannan hanyoyi to da ikon Allah zaku samu nasara.

No comments:

Post a Comment