Saturday, 12 January 2019

Yadda Yalo Yake da Amfani a Jikin Dan Adam

        
(GARDEN EGG)

Yalo dangi ne daga cikin kayan ganye, wanda yawancin amfanin da kayan marmari suke yi shima yalo yana yi. Anan zamu duba amfanin yalo da kuma muhimmancin sa a jikin mu. Bazai yiwu mu kawo duka ba, to amma zamu tsakuru kadan daga cikin amfanin sa.


1. Daga cikin amfanin yalo, yana taimakawa wajen matsaloli na hanta, yana da kyau masu matsaloli irin wannan su dinga cin yalo akai a kai.

2. Idan kana da matsalar ido kuma ka rasa inda zaka saka ranka, to shawara mai kyau ka yawaita cin yalo, domin yana taimakawa matuqa wajen gyaran ido.

3. Yalo yana da amfani matuqa wajan rage yawan sikarin da yake jikinka/ki, hakan zai rage matsalar ciyon sigari sosai.

4. Cin yalo yana kawar da yawan kitsen dake jikin dan adam, wanda yake tottoshe hanyoyin jini da sauransu.
5. Yalo yana taimakawa mace mai ciki domin bawa matar da danta cikakkun sinadaran da suke buqata wajan lafiyar su.

6. Abinda zai bamu sha’awa game da yalo shine, yana da amfani sosai wajan yaqi da cutar nan da kowa ke gudu wato cutar ciwon daji.

7. Amfanin yalo bai tsaya anan ba, yana da amfani matuqa wajan taimakawa masu son su rage qiba, domin yawan cin sa kan saka mutum ya rage qiba sosai.

No comments:

Post a Comment