Tuesday, 22 January 2019

Amfanin agwaluma a jikin dan adamMutane da dama suna son shan agwaluma, musamman mata,to abin tambayar anan shine, shin agwaluma tana da amfani a jikin mutum ko bata dashi? Da yawa suna sha saboda jin dadin rayuwarsu, wasu guma saboda tsaminta, wasu kuma basu da wani dalili na shan nata. To koma menene dalilinka, yanzu zamu ji amfaninta da kuma muhimmancinta akaan lafiyar mu.

1. Agwaluma tana taimakawa kwaran gaske wajan rage nauyin mutun, idan kana tinanin kayi nauyi da yawa, ka suwo agwaluma kai ta sha, zaka ga abin mamaki.

2. Ga mata masu ciki kuma, agwaluma tana taimaka musu matuqa gaya wajan rage musu yunqurin amai, wato tsamin da take dauke dashi yana sakawa su daina jin amai a ko da yaushe.


3. Agwaluma tana maganin rashin kashi, ma’ana ga wanda ya kasa yin bayan gida, agwaluma zata taimaka mai don yin sa, saboda zaqi da kuma tsamin da take dashi a hade.

4. A gargajiyance ana amfani da ganyen agwaluma domin maganin gudawa da kuma ciwon ciki.

5. Ana amfani da Bargon bishiyar agwaluma don maganin shawara da zazzabin cizon sauro

1 comment: