Friday, 28 December 2018

Yadda zaka dinga ganin hirar da budurwarka take a WhatsApp ba tare da ta sani ba

ganin hirar whatsapp

A wannan lokacin zamu koyi yadda zaka buɗe whatsapp ɗin abokinka, budurwarka, da koma wa kake so ta hanyar komputa ba tare da sun sani ba. Amma fa ka sani cewa kula/buɗe hirar da ba taka ba a WhatsApp ya saɓa dokar gudanarwa ta kafanin, saboda haka yana da kyau ka nemi izinin mutumin kafin kayi.

1. Buɗe WhatsApp dake kan wayar budurwar. Yana da farin alamar kira a cikin koren alamar magana.
Amma idan babu a cikin wayar, sai a ɗauko a play-store ko kuma a tura ta Xender.

2.Matsa Saituna ‘settings’ a (iPhone) ko digo guda uku na saman hannun dama a (Android). Zaɓin Saitunan iPhone yana nan cikin kusurwar dama a ƙasa.
Amma idan WhatsApp ya buɗe hirar ƙarshe ne, sai ka fara danna "Back" a saman kusurwar hagu na shafin hirar.
3.Sai ka danna ‘WhatsApp Web/Desktop’. Amma a android zaka ga ‘WhatsApp Web’

4.Bude shafin yanar gizon WhatsApp akan komfutarka. Zaka ga wani akwati mai baƙi-baƙi da fari a kusa da tsakiyar shafin; wannan itace QR code ne, wanda zaka haska ta hanyar amfani da kemarar wayar.

5. Sanya kemarar wayar budurwar a QR code ɗin. Dole ne fuskar  wayar ya fuskance ka, yayin da kemarar wayar sai ta fuskanci QR code ɗin dake kan komputar.

6. Jira komputar ta gama dubawa. Amma idan kaga ta kasa dubawa, sai ka matsar da wayar zuwa gaban komputar da kyau.

Da zarar an ƙaddamar da lambar QR zaka ga saƙonnin da aka tura ta waya sun fito a komputar. To daga nan kuma duka wani sabon saƙo da ka tura kaima zai shigo maka.

No comments:

Post a Comment