Thursday, 27 December 2018

Yadda Akeyin Amai a cikin mota

amai a mota

Yadda ake yin amai idan kana mota
Shin kana tuƙa motarka ne kuma kana jin cewa baka da lafiya? Yin amai idan baka da lafiya abu ne mai yiwuwa sosai. Saboda haka, yana da kyau kasan abinda ya kamata kayi.
Hanya ta Ɗaya
Idan ka tsammanin Matsalar

1. Ka guji yin tuƙi. Akwai abinda ake kira da ‘motion sickenss’ da turanci. Ita wannan rashin lafiyar tana faruwa ne idan kana tafiya a cikin mota ko jirgin ruwa. Tana zuwa ne da tashin zuciya da kuma yin amai, wasu lokutan kuma da jin zazzaɓi. Idan kasan hakan yana faruwa dakai, to abu mafi a’ala shine kar ka zama mai tuƙin ko kuma kar kayi tafiyar ma gaba ɗaya.

2. Yi amfani da magungunan da suke hana amai da kuma tashin zuciya kafin yin tafiya. Akwai magunguna kamar su Dramamine ko Meclizine waɗanda zasu taimaka wajen hana amai da tshin zuciya. Kuma ana iya siyar dasu ba tare da takardar asibiti ba. Amma ka tabbatar cewa baka sayi mai sa bacci ba Bayan nan akwai magunguna kamar Pepto-Bismol. Ka tambayi likita domin sanin maganin daya dace kayi amafani dashi.

3. Ka ajiye chin gum da ledar amai a motar. Idan kasan zaka iya yin amai a cikin motar, sai ka shiga da alewa jo chin gum domin su rage maka tashin zuciya. Sannan kuma kar ka manta da ledar amai, saboda tsaro.

4. Ka ci chitta kafin ayi tuƙi. Chitta tshohuwar mangani ce na amai da tashin zuciya. Bincike ya nuna cewa tana taimakawa wajen motion sickness. Amma fa idan kana shan wasu magungunan ciwon jini kamar aspirin, yana da kyau ka tambayi likita kafin kayi amfani da citta, domin tana ƙara gudun jini da zubar sa.

5. Ka koyi alamomin hanya kafin kayi tafiya. Idan kaine zakayi tuƙi ta yana da kyau ka san ƙa’idojin hanya da kuma alamomin su. Hakan zai taimaka maka idan kana buƙatar ka tsaya ko kuma jin amai. Kar ka dinga tuƙi a tsakiyar titi, sannan kuma ka guji manyan hanyoyi. Ka tina cewa duk lokacin da kaji kanak a ya fara ciwo, to hakan alama ce da take nuna maka cewa ya kamata da tsaya da tafiyar.
Hanya ta Biyu:
Magance tashin zuciya nan take.

1. Ka faɗakar da fasinjojinka. Ka bari fasinjojinka su san idan an kana jin tashin zuciya ko amai. Wataƙila akwai masu abinda zasu taimaka dashi, ko kuma akwai wanda zai iya tuƙa motar. Abu mai amfani anan shine bazasu tsorata ba idan sukaga kayi aman ba.

2. Yi ƙoƙarin tsayawa a hankali. Abu mafi mahimmanci shineka zamana kana da iko da motar kuma ka tabbatar da lafiyar ka, fasinjojin ka, da sauran motocin dake tafiya akan hanyar. Kayan jikin ka ba wani abin damuwa ne sosai ba. Idan zaka tsaya, kayi ƙokarin tsayawa ahankali. Kar ka damu da yadda sauran masu tuƙi zasu kalle ka idan kana amai. Da zarar kaji amai sai kayi ƙokarin tsayawa domin kayi shi a geen titi.

3. Idan kana gudu sai kayi hankali. Kar ka tsaya a tsakiyar titi ko kuma kayi ƙokarin shiga gefen titi, domin kuwa sauran motoci basu san me yake faruwa ba. Kada ka shiga cikin rabuwar tsakiya a kan titi ko hanya.

4. Kayi aman a wajen motar idan hakan zai yiwu. Da zarar ka samu ka tsaya a gefen titi, sai kayi sauri ka bude kofa domin kayi a waje. Amma idan baka sami damar tsayawa ba, sai ka dauke kafar ka daga kana totir, sannan ka dora ta akan birki domin gudun ta kawana, sai kayi aman a haka.

5. Kayi aman kai tsaye. Idan ka kasa tsayawa, abu mafi mahimmanci shine kayi aman kai tsaye, kar k durkusar da kanaka, ko kuma ka dauke idonka daga kan titi. Da kayi hatsari, gwara ka bata kayan jikinka ko kuma cikin motarka.
A takaice ka lura da wadannan abubuwan
* Ka guji yin tuƙi.
* Yi amfani da magungunan da suke hana amai da kuma tashin zuciya kafin yin tafiya.
* Ka ajiye chin gum da ledar amai a motar.
* Ku ci chitta kafin ayi tuƙi.
* Ka koyi alamomin hanya kafin kayi tafiya.
* Ka faɗakar da fasinjojinka.
* Yi ƙoƙarin tsayawa a hankali.
* Idan kana gudu sai kayi hankali.
* Kayi aman a wajen motar idan hakan zai yiwu.
* Kayi aman kai tsaye.

No comments:

Post a Comment