Tuesday, 25 December 2018

Yadda Ake Sawa Jiki Ya Dinga Kamshi koda Yaushe

kamshin jiki
* Da farko a zuba lalle a tukunya a sa ruwa sannan a ɗora a kan wuta ya dahu sosai.
- Idan ya gama dahuwa sosai sai a sauke, a tace shi, sannan a cire garin lalle gefe.
- Sai a mayar da ruwan kan wuta, a rage wuta sai a kawo madarar turare na sandal bakhur, damarar Ledus da madara Musk, sannan a bari ya tafasa sosai.
- Sannan a sauke, idan ya huce sai ki nemi jarka ko galan mai cin lita hudu ki juye a ciki.
- Duk lokacin da ki kayi wanka, in kin gama sai ki kawo wannan haɗin ki zuba kaɗan a bokiti, sai ki ƙara ruwa kaɗan.
- Sai ki ɗauraye jikinki da shi, kar ki goge jiki ki bar shi ya bushe, za ki sha mamakin yadda kamshin zai zauna a jikinki.
* Sannan kuma ku zamto masu yawan mu'amalla da turare a koda yaushe, in har kun san baku da hanyar wadannan to ku zama masu yawan sa turaruka a wurare shida kullum a jikin ku.
- Bayan kunnenku
- Dantse
- Sharaba
- Wuya
- kasan nono da sauransu.

* Gaban ku kuma ku dan samu auduga ku jikata da madarar misk (Aisha) sai a dinga matsi dashi, haka zaisa shima gabanki (farji) ya dinga ɗiban kamshi duk lokacin da maigida yakai ga wurin.
* Macen da take so ta riƙa yin ƙamshi mai ɗaukar hankali sai ta nemi:
- Kafi amarya qamshi
- Garin ambar.
- Garin miski.
- Garin kaninfari.
- Kafun-kafun.
Sai ta cakuɗasu a cikin baslilin (Vaseline) ta ringa shafawa. Duk inda kika je to gurin zai dinga qamshi ba za'a so ki tashi ba.

No comments:

Post a Comment