Sunday, 30 December 2018

Yadda Ake Hada Zobo A Mintuna Goma


Lemon zobo ko kuma ce lemon zoborodo abinso ne sosai a wajen mutanen Nigeria ba wai hausawa kawai ba. Saboda haka yana da kyau mu koyi yadda ake hada wannan lemon a mintuna kadan musamman idan munyi baki.

Amma kafin mu fara bayani, yana da kyau musan amfanin zobo a jikin mu.
- yana dauke da sinadarin Vitamins kamar C.
- yan rage hawan jini.
- yana rage zazzabi da zafin jiki.
- ya bada kariya da cututtukan hanta
- yana bada kariya daga cutar jeji.
A lura da cewa baa fiya son mata masu ciki su dinga shan zobo ba saboda yana kara gudun jini wanda zai iya kawo alada, daga nan kuma a sami zubewar ciki.

Abubuwan da ake bukata:
Zobo
Abarba ko kuma bawonta
Citta
Sukari
Yadda ake hadawa:
- abu na farko shine a wanke zobon da ruwa domin a cire kurar dake jikinsa. Amma kar a damu koda anga kalar zobon tana zuba, wannan ba matsala bace babba.
- bayan ya wanku sosai, sai a yayyanka arbarba, ko kuma a wanke bawon abarbar a ajiye a gefe daya.
- Daga nan kuma sai a yayyanka tafarnuwa da citta zuwa kanana a jiye a gefe daya.
- sai a sami tukunya a zuba zobon da aka wanke, sannan sai abarbar da aka yanka ko kuma bawonta, sai a zuba tafarnuwa da citta. Sai a zuba ruwa ya rufe kayan da aka zuba.
- a rufe tukunyar sannan a dora akan wuta. A bari ya tafasa har zuwa mintuna goma zuwa talatin.
- bayan nan kuma sai a sauke daga kan wuta sannan a ari ya huce kafin a tace shi.
- bayan ya huce sai a sami rariya ko dankwalin tata domin a tace ruwan zobon.
- sai a zuba kankara sannan a zuba sukari.
- daga nan kuma sai a sha.

A lura:
- zaa iya shan zobon da zafinsa a matsayin shayi. Wasu mutanen ma sunfi sonsa a haka.
- zaa iya saka citta da yawa domin yayi yaji sosai. Wasu ma suna zuba barkono a ciki.No comments:

Post a Comment