Thursday, 27 December 2018

Yadda Ake Farfesun kifi

farfesun kifi

Abubuwan da ake bukata:
Kifi
Garin yaji ko tarugu nikakke,
citta
Kanunfari
masoro
tafarnuwa
albasa
citta
thyme
curry
gishiri
maggi
nutmeg
cray 
Yadda ake hadawa:
- a wanke kifin sosai, idan ana gudun ƙarni ma za'a iya amfani da toka ko kuma lemon tsami wajen wanke shi.
- Bayana nan sai a sami tukunya mai kyau wadda babu komai a ciki, a zuba kifin.
- Sai kuma a zuba gishiri, maggi, albasa da tafarnuwa.
- Abarshi ya dahu zuwa kamar mintuna goma.
- Bayan an gama abubuwan dana ambata a baya, sai a zuba yaji a ciki, sannan a zuba garin citta ko kuma busasshhiya. Daga ƙarshe kuma sai a zuba kori domin ƙamshi.
- Idan akwai wasu kayan ƙamshin ma za'a iya ƙarawa a ciki sai a bari kifin a wuta har sai ya dahu.
- A lura kar a bari farfesun kifin ya dahu lugub har ya fara farfashewa.
- sannan kuma a kara lura da yawan ruwan da za'a zuba a ciki. Abin nufi anan shine kar ruwa yayi yawa.
- Sannan ba'a yawan juya kifi kar sai ya farfashe kafin ki gama. A hankali zaki dinga juya shi saboda kada su farfashe.
- Idan kina son man kuli, za'a iya sakawa. Amma, yawancin mutane basa sakawa.
- Yana da kyau ki tanadi kayan kamshin ki dana lissafo saboda ban rubuta abin da za'a ce ba'a samu a kasuwa ba, wannnan
a saukake zaki samu.No comments:

Post a Comment